Wasiyyar wata yar shekaru 16 da haihuwa gabanin da rasuwarta a Kaduna (Hotuna)

Wasiyyar wata yar shekaru 16 da haihuwa gabanin da rasuwarta a Kaduna (Hotuna)

- Aisha Ibrahim Umar, yar kimani shekaru 16 ta rubuta wata wasiyya kwanaki kadan kafin rasuwar ta

- Wani dan uwan yarinya ya sanar da labarin a shafin zumunta ta Facebook

- Yarinyar ta bukaci iyayenta su gafarta mata

Wata yarinya mai kimani shekaru 16 da haihuwa wanda aka bayyana a matsayin Aisha Ibrahim Umar, ta bar 'yan uwanta da kawaye cikin baƙin ciki bayan da ta rubuta wani wasiyya kafin rasuwarta a jihar Kaduna a ranar Juma'a da ta gabata.

A cewar wani dan uwanta wanda ya sanar da labarin a shafin zumunta ta Facebook, ya ce Aisha ta rubuta wasikar mai ban tausayi kafin mutuwarta. Wasikar wanda ke dauke da sako na gafara da ta'aziyya tare da wasiyya wanda yarinya ta rubuta a cikin harshen Hausa.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Aisha ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba, 2017.

Wasiyyar wata yar shekaru 16 da haihuwa gabanin da rasuwarta a Kaduna (Hotuna)
Aisha Ibrahim Umar

A wasikarta, yarinyar ta nemi iyayensa su gafarta mata yayin da ta karbi wasu saƙonni zuwa ga iyalai, dangi da malamai da 'yan makaranta. Sakon da ya girgiza kowa da kowa.

Wasiyyar wata yar shekaru 16 da haihuwa gabanin da rasuwarta a Kaduna (Hotuna)
Daya daga cikin wasikar Aisha

A wasikarta, yarinyar ta nemi iyayenta su gafarta mata yayin da ta yi wasu saƙonni zuwa ga ‘yan uwanta da malamai da kuma 'yan makaranta. Sakon da ta girgiza kowa da kowa.

Wasiyyar wata yar shekaru 16 da haihuwa gabanin da rasuwarta a Kaduna (Hotuna)
Wasiyyar da Aisha ta rubuta gabanin da rasuwar ta

Aisha a wasikarta kuma ta bukaci 'yan uwanta da malamai su tsaya a kan kabarin ta su yi mata addu'a bayan an binne ta. Ta kuma rubuta jerin sunayen malamai da kawayenta da kuma makarantu waɗanda za a mika wa wasikarta.

Wasiyyar wata yar shekaru 16 da haihuwa gabanin da rasuwarta a Kaduna (Hotuna)
Wasiyyar marigayiya Aisha Ibrahim Umar

Har ila yau, yarinya ta ambaci wadanda ta ke bin bashi, kuma ta bukaci su biya a wasikar.

A cewar rahotanni, mutane suna kai kawo a gidan ita yarinya wanda ke unguwar Badarawa a Kaduna don karanta wasikar da aka ce sun ƙunshi darussa masu muhimmanci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel