Jeranton sunaye 81 cikin 100 na nadin mukamai da shugaba Buhari ya yi a Arewacin Najeriya

Jeranton sunaye 81 cikin 100 na nadin mukamai da shugaba Buhari ya yi a Arewacin Najeriya

A wani sabon jadawali da aka watsa a yanar gizo ya bayyana jerin dukkannin nadin mukamai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tun da ya hau kujerar mulkin kasar nan a shekarar 2015 da ta gabata.

A yadda jaridar Business Day ta wallafa, nadin mukamai 81 cikin 100 shugaba Buhari ya yi su ne a ga yankin Arewacin kasar nan, yayin da sauran yankunan kasar suka kasafta ragowar mukamai 19 a tsakanin su.

Wannan tsari na jeranton sunayen ya bayyana dukkannin mukamai da shugaba Buhari yayi tare da yanki na kowane mukamin ya fito.

Legit.ng ta fahimci cewa, jerin sunayen ya zo ne a daidai lokacin da Sanata mai wakiltar Yammacin jihar Kogi Dino Melaye yake ikirarin cewa, gwamnatin Buhari ta sanya mutane da dama da ba su dace ba a wuraren mukaman su.

Jeranton sunaye 81 cikin 100 na nadin mukamai da shugaba Buhari ya yi a Arewacin Najeriya
Jeranton sunaye 81 cikin 100 na nadin mukamai da shugaba Buhari ya yi a Arewacin Najeriya

Melaye ya kara da cewa, "nade-naden mukamai da Buhari ya yi yana kamanceceniya da mutumin dake sanye da takalman da suka fi karfin sawayen sa, ya kuma ce akwai son kai da son rai da Buhari ya ke yi wajen nadin mukaman".

KARANTA KUMA: Wani Attajiri ya ce bani wuri ga shahararren mai kudin duniya na daya Bill Gates

A yayin haka dai ministan mata sanata Aisha Alhassan, ta tayr da jijiyar wuya a sakateriyar jam'iyyar APC dake Abuja, inda ta ce gwamnatin Buhari ta maishe da mambobin jam'iyyar reshen jihar Taraba saniyar ware.

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel