Wani Attajiri ya ce bani wuri ga shahararren mai kudin duniya na daya Bill Gates

Wani Attajiri ya ce bani wuri ga shahararren mai kudin duniya na daya Bill Gates

Sakamakon bayanan da aka samu a Amazon.com Inc. hannun jari Jumma'a ya tura Jeff Bezos a saman Billionaires Index a karo na farko, ya sa shi a gaban Bill Gates wanda ya kasance mafi tsayi a matsayin mutum mafi arziki a duniya domin fiye da shekaru hudu.

A sakamakon bincike da rahotannin ranar Jumma'ar da ta gabata, Jeff Bezos wanda shine mai kamfanin Amazon.com Inc. ya samu ribar hannayen jari wanda ya yi sanadin sa na hankade attajirin nan Bill Gates daga kujerar sa kuma ya yi daraf a kanta.

Wani Attajiri ya cewa Bill Gates bani wuri
Wani Attajiri ya cewa Bill Gates bani wuri

Wannan dorin dosano da Bezos ya yi akan kujerar shine karo na biyu a tarihin rayuwar sa, wanda hakan ya faru ne watanni uku da suka gabata a watan Yulin shekarar nan.

A wallafar mujallar Forbes, Bezos ya na kimanin dalar Amurka biliyan 89.7 a safiyar ranar Jumma'ar da ta gabata, inda Bill Gates yake da dalar Amurka biliyan 90.1.

KARANTA KUMA: Ko Kadan bani da ra’ayin nadin mukamin hukumar Shari’a – Salami

Legit.ng ta fahimci cewa Bezos mai shekaru 53 a duniya, ya samu ribar dalar Amurka biliyan 28.5 a wannan shekarar.

Sanadiyar ribar hannayen jari da kamfanin Amazon na Bezos ya samu a kasuwancin ranar, ya sanya shi ya habaka zuwa dalar Amurka Biliyan 90.6 inda ya bar Bill Gates a matakin sa na Dalar Amurka biliyan 90.1.

A karshen cin kasuwanni na Amurka a ranar Jumma'a, Bezos yana da tasiri na dolar Amurka biliyan 93.8, dala biliyan 5.1 doriya kenan akan Gates kamar labaran Bloomberg ya wallafa a binciken matsayi na yau da kullum na mutane 500 masu arzikin duniya.

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel