Mai son ganin karshen duniya, ya taba Koriya ta Arewa

Mai son ganin karshen duniya, ya taba Koriya ta Arewa

Rahotanni sun kawo cewa wani sabon bincike da aka aiwatar akan karfin sojin kasar Koriya ta Arewa, ya sanya zukatan kasashen yamma cikin dar-dar, bayan ganowa a akayi cewa kasar ta tsere masu.

An bankado cewa, kwana daya kacal da fara yaki da Koriya ta Arewa, illahirin al'umomin kasashen Koriya ta Kudu, Japan da Guwam za su bakunci lahira, ba tare sun samu damar daukar makami ba.

Domin karfin bama-baman da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong ya tanada sun zarce na wadanda Amurka ta jefa a Nagazaki da Hiroshima sau 16.

Bayan makamai masu guba,tana da makamai masu linzami dubu 10, manyan makamai masu cin zango kusan dubu.

Mai son ganin karshen duniya, ya taba Koriya ta Arewa
Mai son ganin karshen duniya, ya taba Koriya ta Arewa

KU KARANTA KUMA: Atiku ya yaba ma Buhari kan sanya hannu da yayi a dokar NEDC

Har ila yau tana da rokokin da ka iya rugurguje Koriya ta Kudu a cikin kiftawar ido, akalla sau 750.

Wani malamin jami'ayyar Troy ta Koriya ta Kudu ya tabbatar da cewa makaman da Kim Jong Un yake da su, ba wai Amurka ba, suna iya kawo karshen duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel