Sunayen sanatocin da suka tallafawa ma’aikatan jihar Kogi da buhunar shinkafa

Sunayen sanatocin da suka tallafawa ma’aikatan jihar Kogi da buhunar shinkafa

- Senatocin sun tallafawa ma'akkatar gwamnatin jihar kogi akan rashin biyan su albashi

- Melaye ya ce ma'akatar gwamantin jihar Kogi sun zama kamar yan gudun hijira a jihar su

-Senata Dino Melyae ya ce tallafin shinkafa zai rage yunwa a jihar

Rashin biyan albashi yasa senatoci 40 sun tallafawa ma’aikata gwamnatin jihar Kogi da buhunar shinkafa 1,260.

Gwamantin jihar Kogi karkashin jagorancin Yahaya Bello ta rike wa ma’aikatar gwamnatin jihar Albashin su na watanni 12.

Senata mai wakiltar mazabar yammacin Kogi Dino Melaye ya ce tallafin shinkafar zai rage yunwar da azzalumar gwamnatin Yahaya Bello ta jnayo wa mutanen jihar.

Senata ya ce ma'aikatar jihar Kogi sun zama kamar yan gudun hijira a cikin jihar su.

Sunayen senatocin da suka tallafawa ma’aikatan jihar Kogi da buhunar shinkafa
Sunayen senatocin da suka tallafawa ma’aikatan jihar Kogi da buhunar shinkafa

Sanata Melaye ya ce, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu ya ba da tallafin buhunar shinkafa jaka 100 yayin da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ba tallafin buhunar shinkafa 30.

KU KARANTA : Buhari yana daukan alhakin saukin kan Goodluck Jonathan – Matasan Ijaw

Sanata Philip Aduda (30), Tayo Alasoadura (20), Obinna Ogba (20), Sen Bala Ibn Na'Allah (20), Ibrahim Gobir (50) Atai Aidoko Ali (70) da Peter Nwaoboshi(30).

Sanata Umaru Kurfi (20), Adamu Aliero (50), Danjuma Goje (50), Bayero Nafada (30), Sam Anyanwu (20), Buruji Kashamu (50), Laa Danjuma (15), Rose Oko (20) da Fatima Raji Rasaki (10).

Sauran su ne Sanata Suleiman Adokwa (10), Ben Bruce (jakuna 10) Jerry Oseni (jaka 20), Isa Shuaibu (jakuna 40), Ahmed Ogembe (30), Albert Bassey (20), Mustapha Bukar (20) ), Yusuf A. Yusuf (jaka 15) da Buka Kaka Bashir (20).

Sanata Abdullahi Ginmel (20 ), Malam Ali Wakili (20), Ovie Omo-Agege (50), Barau Jibrin (10), Adeola Solomon (20), Rafiu Ibrahim (30), Stella Oduah (30), Sonni Ogbuoji (10 ), Shaaba Lafiaji (20 ), Francis Alimekhena (20), Matthew Urhoghide (20) da Biodun Olujimi (20).

Melaye ya ce Sanata Philip Aduda ya ba da kyautar takalma 10 ga manoma a jihar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci hukumar ba da agajin gaggawa da ta aika kayan agajin ga ma'aikatan gwamnati jihar Kogi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel