Maina: Saura kuma a tsige Malami da Dambazzau Inji PDP

Maina: Saura kuma a tsige Malami da Dambazzau Inji PDP

- Jam'iyyar PDP ta fadawa Shugaban kasa Buhari ya tsige wasu Ministoci

- Ministocin sun hada da Ministocin harkar cikin gida da na shari'a a Kasar

- Ana zargin su da yin kutun-kutun wajen dawo da Abdurrasheed Maina aiki

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Jam'iyyar adawa ta PDP ta nemi Shugaban kasa Buhari ya sauke wasu Ministocin daga cikin Ministocin sa.

A game da dawowar Abdurrasheed Maina bakin aiki, inda har aka kara masa matsayi, PDP ta nemi a sauke Ministan cikin gida Abdulrahman Danbazzau tare da Ministan shari'a Abubakar Malami wanda ake ganin akwai hannun su a cikin maganar.

KU KARANTA: Buhari ya kori Maina daga bakin aiki

Sakataren yada labarai na Jam'iyyar Prince Dayo Adeyeye ya bayyana wannan inda ya nemi Hukuma ta kama Maina tare da hukunta sa. PDP ta ce dole mu zaba masu fadawa kan mu gaskiya duk da bambancin siyasa. Adeyeye yace ana zargin Maina da yin gaba da kudin Jama'a.

PDP ta zargi Gwamnatin APC da kokarin rufawa marasa gaskiya asiri inda tace maganar banza ce kurum ace wai wata Kotu ta wanke Maina a fadin kasar nan. Dazu dai Shugaban kasar ya kora Abdurrasheed Maina daga aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel