An kama wani babban jami'in kungiyar ASUU da laifin karbar cin hancin Naira dubu 50 hannun dalibai

An kama wani babban jami'in kungiyar ASUU da laifin karbar cin hancin Naira dubu 50 hannun dalibai

Labaran da muke daga majiyoyin mu samu a kamfanin mu yanzu haka na nuni ne da cewa jami'an hukumar gudanarwar jami'ar jihar tarayyar dake Legas ta kori ma'aikatan jami'ar da suka hada da masu koyarwa da wadanda ma basu koyarwa har 17 bisa laifuffuka da dama.

Haka ma kuma dai mun samu cewa a cikin wadanda hukumar gudanarwar jami'ar ta kora daga aikin sun hadda da shugaban kungiyar nan ta malaman jami'oi watau ASUU da kuma ma mataimakin sa kamar dai yadda mai magana da yawun jami'ar ya shaida mana.

An kama wani babban jami'in kungiyar ASUU da laifin karbar cin hancin Naira dubu 50 hannun dalibai

An kama wani babban jami'in kungiyar ASUU da laifin karbar cin hancin Naira dubu 50 hannun dalibai

KU KARANTA: Jami'an EFCC sun zagaye gidan Abdurrasheed Maina

NAIJ.com dai har ila yau ta samu kuma cewa cikin wadanda korar ta shafa hadda wasu ma'aikatan jami'ar da masu koyarwa mutum biyu sai kuma wasu da dama da aka rage wa girma bisa laifuffukan da aka kama su da su dabandaban.

Da yake karin haske game da musabbabin dalilan korar malaman jami'ar mai magana da yawun jami'ar ya bayyana wa majiyar ta mu cewa an kama shugaban kungiyar ne da laifin karbar cin hancin Naira dubu 50 daga hannun dalibai yayin da shi kuma mataimakin kungiyar aka kama shi da laifin canza sakamakon wasu dalibai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, to tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel