Zaben 2019: Kimanin 'yan Najeriya miliyan 80 ne zasu yi wa yan siyasa hisabi

Zaben 2019: Kimanin 'yan Najeriya miliyan 80 ne zasu yi wa yan siyasa hisabi

Hukumar dake da alhakin gudanar da zabuka ta gwamnatin tarayya a Najeriya ta bayyana cewa akalla mutanen Najeriya sama da miliyan 80 ne za su iya kada kuri'a a zaben gama-gari na 2019 mai zuwa.

Shugaban hukumar ta zaben watau INEC a takaice Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a karshen mako a garin Abuja yayin da ya karbi bakucin tawagar nahiyar turai da ke da alaka da sahihan zabuka da sauran kungiyoyin sa kai da ma wasu masu ruwa-da-tsaki.

Zaben 2019: Kimanin 'yan Najeriya miliyan 80 ne zasu yi wa yan siyasa hisabi

Zaben 2019: Kimanin 'yan Najeriya miliyan 80 ne zasu yi wa yan siyasa hisabi

KU KARANTA: Shugaba Buhari na shirin sake ficewa zuwa wata kasa

NAIJ.com ta samu kuma cewa shugaban INEC din Farfesa Mahmoud ya kuma bayyana irin namijin kokarin da hukumar ke yi tare kuma da aiki tukuru ba dare ba rana don ganin zabukan da ke tafe sun fi na baya inganci.

Haka ma dai shugaban na hukumar ya kuma bayyana cewa a cikin 'yan kwanakin nan ne hukumar zata fitar da kasafin kudin ta da take bukata domin gabatar da sahihin zaben 2019.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel