Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya bayar da umurnin korar Abdulrasheed Maina da gaggawa

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya bayar da umurnin korar Abdulrasheed Maina da gaggawa

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da wani umurni na gaggawa da a kori babban ma'aikacin nan na Gwamnatin tarayya da yanzu haka yake a matsayin Darakta a ma'aikatar dake kula da harkokin cikin gida.

Wannan umurnin na shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Mista Femi Adesina ya fitar inda ya bayyana cewa shugaba Buhari din ya bayar da umurnin ne da safiyar yau Litinin 23 ga watan Oktoba.

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya bayar da umurnin korar Abdulrasheed Maina da gaggawa

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya bayar da umurnin korar Abdulrasheed Maina da gaggawa

KU KARANTA: Sule Lamido ya bayyana ra'ayin sa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2019

NAIJ.com ta samu kuma cewa haka zalika shugaba Buhari din ya kuma bukaci karin bayani daga shugaban ma'aikata na gwamnatin tarayya game da yadda akayi har aka maido shi aiki a asirce duk kuwa da irin zargin almundahanar da ake yi masa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari na ta shan suka daga jama'a da dama tun bayan da labarin maida Abdurrashid Maina ya bazu inda masu sharshi ke cewa bai kamata ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel