EFCC: Abdurrasheed Maina ya fara ganin ta kan sa bayan an auka gidajen sa

EFCC: Abdurrasheed Maina ya fara ganin ta kan sa bayan an auka gidajen sa

- Hukumar EFCC ta dura gidan tsohon Shugaban harkar fansho

- Hakan na zuwa ne bayan umarnin da Shugaban kasa ya bada

- Yanzu haka ba a san inda Abdurrasheed Maina ya shige ba

Labari ya zo mana daga Jaridar Premium Times cewa Jami’an EFCC sun zagaye gidan Abdurasshed Maina bayan umarnin Shugaba Buhari.

EFCC: Abdurrasheed Maina ya fara ganin ta kan sa bayan an auka gidajen sa

EFCC na neman Abdurrasheed Maina

Manyan jami’an Hukumar EFCC da ke yaki da yi wa tattalin kasa zagwon-kasa sun zagaye katafaren gidan tsohon Shugaban wata gidauniyar fansho da aka bude a kasar Abdurrasheed Maina da la’asar dinnan. Gidan dai yana Layin Hamisu Musa ne a Unguwar Jabi da ke Birnin Abuja.

KU KARANTA: Buhari ya bukaci a tsige Maina ba tare da jinkiri ba, ya nemi ayi bincike a kan sa

Kamar yadda mu ka ji gidan da ake magana ya kai Dala Miliyan 2 wanda dama tun ba yau ba ake neman Alhaji Maina inda ya sulale ya bar kasar. A karshen makon nan ne mu kaji cewa an dawo da Maina ofishin sa har da kara masa matsayi wanda ya sa Shugaban kasa Buhari yace sai ya ji wanda ya tsaya masa.

Mun samu labari kuma dai ba da dadewa ba Jami’an na EFCC za su auka wani gidan Alhaji Maina da ke Unguwar Kado a Babban Birnin Tarayyar na Abuja. Yanzu dai Maina yayi dabo ba a san inda ya shiga ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel