Buhari na shiri don sake wani tafiya mai muhimmanci

Buhari na shiri don sake wani tafiya mai muhimmanci

- Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari zai bar kasar a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba zuwa Niamey, jumhuriyar Nijar

- Shugaban kasa Buhari ya shirya tsaf don halartan wani taro na yankin Afrika ta Yamma

- Shugaban kasar zai samu rakiyan ministar kudi na Najeriya, Kemi Adeosun da kuma gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele

A ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa Niamey, jumhuiyar Nijar don halartan wani taron kudi na Afrika ta yamma.

An sanar da hakan ne a wata sanarwa daga Femi Adesina, maiba shugaban kasa shawara na musamman a shafukan zumunta da kafofin watsa labarai.

Kasashen dake cikin wannan taron sun hada da ‎Nijeriya, Cote d'Ivoire, Ghana da Nijar.

KU KARANTA KUMA: Ba na kewar yin fina-finan Kannywood - Mansura Isa

Ministan kudi, Misis Kemi Adeosun da gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, zasu yi ma shugaban kasar rakiya zuwa taron.

Shugaba Buhari zai dawo Abuja a wannan rana bayan taron.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel