Siyasa: Gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin

Siyasa: Gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin

- Gwamnonin yankin kudancin Najeriya za su gana a Legas a ranar Litinin

- Wannan taron gwamnonin ita ne karo na 12 na irin wannan taro

- Ana sa ran gwamnonin za su tattauna matsalolin da ta shafi yankunan su da kasar gaba daya

Gwamnonin 17 daga yankunonin kudu maso yamma da kudu maso gabas da kuma kudu maso kudu za su hadu a Legas a ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba don tattauna batutuwa na kasa da kuma karfafa dangantakar da ke tsakaninsu.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, taron yana zuwa ne bayan shekaru 12 na irin wannan taro.

Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar Legas (SSG), Mista Tunji Bello ya bayyana, ya ce gwamnonin Legas, Akinwunmi Ambode da takwaransa na Akwa Ibom, Emmanuel Udom za su jagoranci taron.

Siyasa: Gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin

Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode

A cewarsa, ana sa ran gwamnonin za su yi matsayi daya a kan batutuwa da ta shafi fashi da makami, sace-sacen mutane, musayar ikon, batutuwa na kasa da sauransu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Turkiyya

"Idan dai baku manta ba, an kaddamar da taron ganawar gwamnonin yankin kudancin Najeriya ta farko a Legas a shekara ta 2001 a karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu", in ji Bello.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel