Ribar da Najeriya zata girba daga ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Turkiyya

Ribar da Najeriya zata girba daga ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Turkiyya

Shugaba Buhari yana kasar Turkiyya a wata ziyarar aiki da ya kai domin halartar taron kasashen D-8. Wannan ita ce ziyarar shugaba Buhari ta farko a kasar Turkiyya tun bayan hawansa mulki.

Ga wasu daga cikin ribar da ake ganin Najeriya zata samu daga wannan ziyara da shugaba Buhari ya kai kasar ta Turkiyya:

Tsaro da Hadin gwiwa wajen yakar ta'addanci: Kasashen Najeriya da Turkiyya sun amince da hada kai domin kawo karshen safarar makamai da yaki da ta'addanci.

Ribar da Najeriya zata girba daga ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Turkiyya

Ribar da Najeriya zata girba daga ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Turkiyya

Hakazalika kasar Turkiyya ta tattauna da Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, da shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali, domin tabbatar da an kawo karshen safarar mugayen makamai zuwa Najeriya.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin bawa mai laifin cin hanci mukami a sirrance

Masana'antu, Zuba jari, da harkar Sufuri: Kasashen Najeriya da Turkiyya sun yanke shawarar kara bunkasa alakar kasuwanci domin habaka tattalin arziki, musamman ganin cewar akwai karancin kulluwar harkokin kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar D-8.

Kasar Turkiyya dai nada kamfanoni 48 a Najeriya da karfin jarinsu ya kai Dala miliyan 600.

Hakazalika a bangaren sufuri, kasar Turkiyya ta nemi karin yawan adadin kamafanonin jirgin sama na kasarta da zasu ke jigila a Najeriya.

Ribar da Najeriya zata girba daga ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Turkiyya

Ribar da Najeriya zata girba daga ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Turkiyya

Bangaren ilimi da Lafiya: Kasar Turkiyya dai an shiada cewar taci nasara a wadannan bangarori da yanzu tayi alkawarin tallafawa Najeriya ta bukasa nata.

A cikin wasu kwanaki masu zuwa ne kasar Najeriya data Turkiyya zasu rattaba hannu a kan wadannan kudirori domin fara aiki da su.

DUBA WANNAN: Dubi hotunan wata budurwa 'yar kwalisa da 'yan fashi suka yiwa wal-mukalifatu

Tawagar shugaba Buhari da ya isa da ita Kasar Turkiyya ta hada da matarsa, Aisha Buhari, Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, Ministan tsaro, Mansur Dan Ali, Ministan ilimi, Adamu Adamu, da na Masana'antu da harkokin zuba jari, Okechukwu Enelamah.

Ragowar sun hada da Mai bawa shugaban kasa shawa a fannin tsaro, Babagana Munguno, Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali, da jakadan Najeriya a kasar Turkiyya, Ilyas Sulaiman Paragalda.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel