Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin bawa mai laifin cin hanci mukami a sirrance

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin bawa mai laifin cin hanci mukami a sirrance

- A Shekar 2013 ne hukumar EFCC ta bayyana neman Abdulrashid Maina ruwa a jallo

- Yanzu haka Maina shi ne ke rike da sashen kula albarkatun mutane na ma'aikatar harkokin cikin gida

- Dambazau ya bayyana cewar duk wani zargi kamata yayi a nufi ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka dawo da Maina bakin aiki

Bayan jaridar Premium times ta kwarmata bawa Abdulrashid Maina mukami a sirrance cikin gwamnati, ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, ya fito domin kare dalilin da yasa gwamnati ta bawa Maina mukamin sakataren a ma'aikatar harkokin cikin gida duk da zargin badakalar cin hancin Naira biliyan 2 dake kan sa.

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin bawa mai laifin cin hanci mukami a sirrance

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin bawa mai laifin cin hanci mukami a sirrance

A Shekar 2013 ne hukumar EFCC ta bayyana neman Abdulrashid Maina ruwa a jallo bayan da ya buya domin gujewa binciken badakalar cin hanci ta kudin 'yan fansho da adadinsu yakai Naira biliyan 2. Binciken jaridar ya tabbatar cewar har yanzu maina na cikin jerin mutanen da hukumar ta EFCC ke nema.

DUBA WANNAN: Gwamna Almakura na yunkurin sayar da gidan gwamnatin jihar Nasarawa - Labaran Maku

A wani bayani da sakataren minista Dambazau, Ehisienmen Osaigbovo, ya tabbatar da cewar yanzu haka Maina shi ne ke rike da sashen kula albarkatun mutane na ma'aikatar harkokin cikin gida, kuma an turo shi ma'aikatar ne kwana biyu da suka wuce daga ofishin shugaban kula da ma'aikata na kasa biyo bayan ritayar mai rike da mukamin da aka nada Maina.

Dambazau ya bayyana cewar duk wani zargi kamata yayi a nufi ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya da suka dawo da Maina bakin aiki, sannan bayanin nasa bai bayyana cewar ko yana sane cewar Maina na fuskantar tuhuma a hannun hukumar EFCC ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel