Har yanzu Shugaba Buhari ya gaza nada wasu muhimman mukamai a Gwamnati

Har yanzu Shugaba Buhari ya gaza nada wasu muhimman mukamai a Gwamnati

- Tun kafa Gwamnati kawo yanzu Shugaba Buhari bai nada wasu mukamai ba

- Wannan ya sa ake samun cikas wajen gudanar da sha'anin Gwamnati a Kasar

- Daga ciki wadannan akwai Hukumar RMFAC, NPC, FCC, INEC da FCSC

Jaridar Daily Trust tayi wani nazari inda ta gano akwai mukaman Kwamishinonin Hukumomin Tarayya har 83 da har yau Shugaba Buhari bai nada ba.

Har yanzu Shugaba Buhari ya gaza nada wasu muhimman mukamai a Gwamnati

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauki lokaci bai nada mukamai ba

Watau tun kafa Gwamnati a tsakiyar 2015 kawo yanzu Shugaban kasa Buhari bai nada wadannan mukamai ba. Wannan ya sa ake samun cikas wajen gudanar da sha'anin Gwamnati a Kasar inda a wasu Jihohin babu aikin da Hukumomin ka iya yayi saboda manyan sun yi ritaya ko wa'adin su ya kare.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai nemi ya zarce a 2019

Kamar yadda rahoton ya zo mana, daga ciki wadannan akwai Hukumar RMFAC mai ware albashin Ma'aikata, da kuma Hukumar NPC ta kidaya, da Hukumar FCC da ke ganin ba a maida wasu saniyar-ware ba a kasar, sannan da Hukumar zabe na kasa da Hukumar da ke kula da Ma'aikatan Gwamnati.

Kwanaki ma dai sai da aka yi ta dauki ba dadi sannan aka nasa Kwanishinonin Hukumar zabe. Wannan ne dai ya sa Majalisa ke neman tursasawa Shugaban kasar ya nada wadannan mukami. Akwai dai mukamai da dama da Gwamnatin Tarayya ta gaza nadawa a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel