Tofa: Wani Dalibi ya maka Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a Kotu

Tofa: Wani Dalibi ya maka Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a Kotu

- Wani Dalibin PhD a ABU ta Zariya ya maka Jami’ar Kotu

- Jamilu Auwalu yana karar Malamin sa Dr. Abubakar Yahaya

- Haka kuma Dalibin ya nemi Jami’ar ta biya sa wasu kudi

Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda wani Bawan Allah mai karatun Di-gir-gir a ABU ya kai wasu Malaman sa Kotu. Ba dai yau aka saba kukan Jami'o'in na matsawa Dalibai lamba ba.

Wani Dalibin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ya maka Jami’ar kara a Babban Kotun Tarayya da ke Garin Kaduna inda ya nemi a biya sa kudi har Naira Miliyan 20 saboda bata masa lokaci da dukiya da su kayi. Za a zauna ne dai a Kotu a tsakiyar watan gobe.

KU KARANTA: An maka wani Dan Najeriya kurkuku a Amurka

Jamilu Auwalu Adam wanda yake karatun PhD watau Digiri na uku a fannin lissafi ya bayyana yadda Dr. Abubakar Yahaya wanda shi ne aka sa ya duba kundin aikin sa ya matsa masa lamba dalilin bai sa sunan sa a aikin sa da ya buga a wata mujalla ba.

Haka kuma Dalibin yana karar Farfesa Babangida Sani wanda yana cikin masu duba aikin na sa. Wannan Bawan Allah ya fara karatun ne a 2014 inda ya nemi a hukunta Malamin na sa don ma bai kai matsayin duba aikin mai Digiri na uku ba kuma a nema masa wani Malamin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel