'Yan wasan fim din Hausa sun marawa Atiku baya a takarar 2019

'Yan wasan fim din Hausa sun marawa Atiku baya a takarar 2019

- 'Yan wasan kwaikwayo a Najeriya na marawa Atiku baya

- Ana tunani Atiku zai tsaya takarar Shugabanci a 2019

- Irin su Fati Muhammad su na tare da babban Dan siyasar

Mun samu labari daga Abu Sidiqu cewa wasu 'Yan wasan fim sun yi wani taro a Garin Kaduna inda har su ka nuna alamun marawa Alhaji Atiku Abubakar baya a zabe mai zuwa.

'Yan wasan fim na Kannywood na marawa Atiku baya bisa dukkan alamu. Irin su Fati Muhammad su ka halarci taron inda aka kara mata girma a harkar. Sauran manyan Taurari irin su Adam Zango da Rabiu Rikadawa da wasu Darektoci ma ba a bar su a baya ba.

KU KARANTA: Rikicin neman kujerar Shugabancin PDP

Sauran wadanda su ka halarci taron a Kaduna sun hada da Abida Mohammed da Fati Washa, Sadiya Gele, Tahir I. Tahir, Shamsu Cash Money, Abbas Sadik, Mama Binta, Binta Kofarsoro, Fati Yola, Fati Mama, Hadiza Kabara, Fati K.K., da dai sauran su.

Ana tunani Wazirin Adamawa Atiku Abubakar zai tsaya takarar Shugabanci a 2019. Kuma da alamu a wajen taron da aka karrama Fati Muhammad sun nuna goyon bayan su ga tsohon Mataimakin Shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel