Tirkashi! Gwamnati ta ce a tattaro mata kudaden da ba'a yi wa asusun bankin su BVN ba

Tirkashi! Gwamnati ta ce a tattaro mata kudaden da ba'a yi wa asusun bankin su BVN ba

- An sa dokar kowa sai ya yi wa asusun bankin sa BVN tun a shekarar 2014

- Har yanzu akwai asusan da ba'a yi musu ba, wanda ya kawo biliyon kudi a ajiye kawai turus

- Gwamnati ta ce a tattaro mata su in ba masu shi

Kotin koli ta kasa ta baiwa gwamnati dama da a tattara mata kudaden asusan bankunan da ba'a yi musu BVN ba. Shugaban lauyoyin kasa, Abubakar Malami, ne ya shigar da wannan neman izinin da yawun gwamnati.

Ana kyautata zaton cewa wadannan kudaden a kalla sun kai biliyoyin Nairori, daloli, da fam-fam — suna zaune a bankuna turus kawai ba'a amfani da su.

Tirkashi! Gwamnati ta ce a tattaro mata kudaden da ba'a yi wa akawun bankin su BVN ba

Tirkashi! Gwamnati ta ce a tattaro mata kudaden da ba'a yi wa akawun bankin su BVN ba

Kotun ta umarci duka bankunan kasa su 19 da jama'a ke ajiyar kudi da su mika wa gwamnati sunayen kowanne asusun da ba'a yi wa BVN ba, da kuma nawa ne a ciki.

A yanzu haka bankuna 16 sun baiyana za su tura, sauran ukun kuma sun yi gum. Ukun sune: bankunan Unity, Wema da Zenith.

Gwamnati ta umarci duka bankunan da su buga sunayen masu asusan, da balas din da ke ciki, a jaridu, da kuma ba su sati biyu don su fito su fadi lallai dalilin me ya sa bai kamata a baiwa gwamnati kudin ba.

DUBA WANNAN: Ko 'yan adawa sun shaida mun samu nasara - Shugaba Buhari

Wannan batu na kotu ya sa shiyyoyi sun yi caa a kan gwamnati a kan bai kamata a tilastawa bankuna su baiyana abin da aka basu ajiya ba.

Shin ko ya zata kaya?

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel