Ko 'yan adawa sun shaida mun samu nasara - Shugaba Buhari

Ko 'yan adawa sun shaida mun samu nasara - Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya gana firaministan kasar Pakistani yau a Turkiyya

- Ya Shaida cewar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ya taimaki Najeriya wajen samun nasarar yaki da ta'addanci

- Shugaba Buhari ya shaida cewar ko masu adawa da gwamnatinsa sun shaida nasarar da ya samu

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ko masu adawa da gwamnatinsa sun shaida nasarar da yake samu, musamman a bangaren tsaron kasa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakane yayin wata ganawa da firaministan kasar Pakistan, Shahid Khakan Abbasi, a taron kasashen D-8 da ake gudanarwa a kasar Turkiyya.

Ko 'yan adawa sun shaida mun samu nasara - Shugaba Buhari

Shugaba Buhari da firaministan kasar Pakistan, Shahid Khakan Abbasi

Da yake karin haske a kan ganawar Shugabannin biyu, mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari ya bayyana cewar hadin gwuiwa ta fannin tsaro tsakanin Najeriya da kasar Pakistan ya taimaka wajen karya lagon mayakan kungiyar Boko haram da suka addabi yankin arewacin Najeriya.

DUBA WANNAN: Hukumar NAPTIP ta yi caraf da wata mata da ta kona kanwar mijinta da tafasashshen ruwa

Hakazalika shugaban ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda kasashen biyu basu kulla harkokin kasuwanci tsakaninsu ba, tare da fatan cewar kasashen zasu bunkasa dangantaka a tsakanin su, musamman a bangarorin da ba na tsaro ba.

A karshe Shugaba Buhari ya mika godiyarsa ga gwamnatin kasar ta Pakistan a kan gudunmawar bayar da horo da kayan aiki da take yi wa sojin Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel