Yadda shuwagabannin Afirika za su magance talauci da rikice-rikice a nahiyar - Shugba Buhari

Yadda shuwagabannin Afirika za su magance talauci da rikice-rikice a nahiyar - Shugba Buhari

- Garba Shehu, mai magana da yawun Buhari, ne ya fitar da wannan jawabi

- Buhari ya yi wannan jawabi ne yayin tattaunawar sa da Shugaban kasar Guinea a Turkey

- Buhari ya yi kira ga shuwagabannin Afirika da su yi magana da murya daya, ba tare da katsalandar din kasashen turai ba, wurin magance talauci da rikice-rikice

A wani jawabin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mai magana da yawun sa, Mista Garba Shehu, ya aikewa Jaridar Punch, Buhari ya bayyana yadda shuwagabannin Afirika za su kawo habakar tattalin arziki, cigaba, aminci da tsaro a Nahiyar.

A jawabin, Buhari ya ce za a kai ga hakan ne idan har shuwagabannin su ka yi magana da murya daya, ba tare da katsalandan din kasashen turai ba wurin magance talauci da rikice-rikice a nahiyar.

Yadda shuwagabannin Afirika za su magance talauci da rikice-rikice a nahiyar - Shugba Buhari

Yadda shuwagabannin Afirika za su magance talauci da rikice-rikice a nahiyar - Shugba Buhari

Buhari ya yi wannan jawabi ne yayin wata ganawar kebe da ya yi tare da Shugaban Kasar Guinea, Alpha Conde, a Istanbul na Kasar Turkey. Conde a halin yanzun shi ne shugaban Kungiyar Kasashen Afirika wato AU.

DUBA WANNAN: Abin mamaki bai karewa! 'Yan mata a Borno sun roki Gwamnatin Jihar ta aurar da su

Buhari ya jaddada karfafa alakar Najeriya da sauran kasashen da ke kungiyar ta AU don shawo kan rikice-rikicen da ke akwai a kasashen Libya da Togo da Kudancin sudan.

Conde a na sa jawabin, ya yabawa Buhari bisa ga yaki da yake yi da cin hanci da rashawa. Ya kuma yawaba Najeriya kan irin kakkyawar wakilcin da ta ke yi wa Afirika a idon duniya.

Conde ya kuma jaddada bukatuwar hadin kan Najeriya da Guinea don habaka tattalin arziki musamman ta bangaren ma'adanai na kasa. Ya yi tinkahon Kasar Guinea ce ke samar da kashi 25 cikin 100 na ma'adanin Bauxite din duniya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel