Kashi daya bisa biyar na dalibai lauyoyi ne suka fadi jarrabawa

Kashi daya bisa biyar na dalibai lauyoyi ne suka fadi jarrabawa

- A watan Agusta ne suka zauna jarrabawar ta karshe

- Dalibai 1700 suka fadi a cikin 6000 da suka zauna ma jarrabawar

- Amma duk da haka, sai an sami ci gaba kan sakamakon bara

Daliban su su 5871 ne suka zana jarrabawar, kuma 1271 ne suka sha kasa, yayin da saura suka shallake, sai dai ko cikin masu tsiran, akwai kusan 300 da suke da kwa-kwai, wato dai gasunan-gasunan, abin da ake kira conditional pass a turance.

Kashi daya bisa biyar na dalibai lauyoyi ne suka fadi jarrabawa

Kashi daya bisa biyar na dalibai lauyoyi ne suka fadi jarrabawa

A cewar rahoton kuma dai, duk da haka, a bana an sami karin masu cin jarrabawar dda kusan kashi 6 bisa dari idan aka kwatanta da ta baya.

Chinedu Ukekwe shugaban yada labarai na makarantar da cibiyarta ke babban birnin tarayya a Abuja ne ya fadi haka ya kuma ce za'a yi bikin yaye daliban da suka yi nasara a watan Nuwambar nan, a ranakun 28 da 29 ga wata.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji fadar shugaban kasa

Yanzu dai dalibai da yawa na karantar lauya, kuma ana samun ci gaba sosai a fannin sharia na kasa, sai dai har yanzu suna saka hullar da turawan mulkin mallaka suka basu a ka.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel