Abinda ya dace da Jonathan shine neman gafara daga Ubangiji da kuma 'yan Najeriya - APC

Abinda ya dace da Jonathan shine neman gafara daga Ubangiji da kuma 'yan Najeriya - APC

- Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo tayiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kaca-kaca

- Jam'iyyar tace ya kamata Goodluck Jonathan yayi tsit da bakinsa kuma ya nemi gafaran Ubangiji da 'yan Najeriya

- Jam'iyyar APC din tayi ikirarin cewa tsohon shugaba Goodluck Jonathan din ne ya jefa Najeriya cikin matsancin halin da muke ciki yanzu

Jam'iyyar APC reshen jihar Ondo tace abinda ya dace da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a wannan lokacin shine neman gafara daga Ubangiji da kuma neman afuwar 'yan Najeriya.

Wannan sanarwan maida martani ne ga kalaman tsohon shugaban kasan inda yayi ikirarin cewa babu abinda gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke tabuka wa illa kareraki da farfaganda.

Abinda ya dace da Jonathan shine neman gafara daga Ubangiji da kuma 'yan Najeriya - APC

Abinda ya dace da Jonathan shine neman gafara daga Ubangiji da kuma 'yan Najeriya - APC

Jami'in hulda da jama'a na jam'iyyar APC reshen jihar Ondon, Abayomi Adesanya yace tsohon shugaban har yanzu bai gama farfadowa dake kayen da yasha a zaben 2015 bane.

DUBA WANNAN: Dan kunan baikin wake Abdulmutallab ya kai karar Ma'aikatar Shari'ar Amurka

Kamar yadda Adesanya yace, ''Babu wata tantama ko kuma musu, kowane dan Najeriya ya sani cewa gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ta jefa kasar nan cikin tsaka mai wuya da ta samu kanta.

''Idan da nine Jonathan, zan tsuke baki na, sannan in cigaba da neman gafara wajen Ubangiji da kuma al'ummar Najeriya a maimakon yin gutsiri tsoma da katsalandan cikin harkokin gwamnati mai ci yanzu."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel