Gwamnatin Buhari ta dawo da wani babban mai laifi bakin aikin sa bayan zargin sata

Gwamnatin Buhari ta dawo da wani babban mai laifi bakin aikin sa bayan zargin sata

- Gwamnatin Buhari ta dawo da Abdurrasheed Maina ofishin sa

- Ana zargin sa da wawushe kudin fanshon Jama'a a lokacin baya

- Ana zargin wasu da na kusa da Shugaban kasar da wannan aiki

Jaridar Premium Times tayi wani bincike na kwa-kwaf inda ta gano cewa Gwamnatin Shugaba Buhari ta wani da ake tuhuma bakin aikin sa.

Gwamnati ta dawo da Abdurrasheed Maina ofishin wanda ake zargi da lamushe kudin fansho a lokacin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan. Hukumar EFCC da sauran Jamia'ai dai su na neman Maina ido rufe wanda ta sa ya bar Kasar.

KU KARANTA: Gudaji kazaure ya soki manufan Shugaba Buhari

A cewar Jaridar Ministan sharia na kasa da kuma Ministan harkokin cikin gida Abubakar Malami da Abdurrahman Dambazzau ne su ka kai su ka kawo aka dawo da wannan mutumi kasar har aka ma kara masa matsayi zuwa Darekta a Ma'aikatar sa.

Hukumar EFCC dai ta bayyana cewa hakan ya ba ta mamaki kwarai ta bakin wani babban Jami'in ta. Gwamnatin Tarayya dai ba ta ce komai ba game da batun. Shi dai Maina tun a lokacin ya karyata zargin da ke kan sa na satar sama da Biliyan 100.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel