Buhari bai cancanci tazarce ba - Junaid Muhammad

Buhari bai cancanci tazarce ba - Junaid Muhammad

- Dakta Junaid Muhammad ya shaida cewa Shugaba Buhari bai cancanci ya sake tsayawa takara a zaben 2019 mai gabatowa ba

- Har yanzu 'yan Najeriya basu ga wani canji a mulkin Buhari ba

- Buhari bai yi ayyukan da zai sa ya tsaya takara ba

Tsohon dan Majalisa Dakta Junaid Muhammad ya fadi wadanda ya kamata a tuntuba don sanin ko cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci tsayawa takara a zaben 2019.

A cewar tsohon dan majalisan ne Buhari bai yi ayyukan da suka isa su saka ya sake tsayawa takara ba. Sannan ya kara da sanarwar cewa ba gwamnoni ne zasu fadi a madadin sa ba in dai har yana da sha’awar ya sake tsayawa takarar a zaben 2019.

Buhari bai cancanci tazarce ba - Junaid Muhammad

Buhari bai cancanci tazarce ba - Junaid Muhammad

'Har yanzu ban ga wasu abubuwa da gwamnonin nan suka yi ba da zamu sake cancanta tsayawa takara. A matsayi na na dan Najeriya har yanzu ba zan bada shaidar wani dan Najeriya da naga rayuwar sa ta canja ba' Junaid Muhammad ya shaida.

'Har yanzu a cikin jam’iyyar APC bamu ga wanin abin arziki da suka tabuka ba, bamu ga alamun cewa suna da zummar aiki ko da gaske suke ba. ‘Yan siyasa sai kaudi suke kamar cin zaben 2019 din abu ne mai sauki, amma ni bana kin yarda da niyyar su da suke da ta mulkin kasa.'

Ya kara da cewa ‘ban ga wani abin arziki da wani ya tabuka ba har da zamu saka masa da zaben sa in ya tsaya takara.’

DUBA WANNAN: Sojoji 6 sun rasa ran su a harin da Boko Haram ta kai a hanyar Dambowa

Da yawan ‘yan Najeriya suna bin son rai ne idan zabe yazo ko kuma su zabi dan garin su da ya kwanta musu, ba wai wanda zai musu aiki ba., hakan ba zai taba sa kasar Najeiya ta cigaba ba.

Idan gwamnoni kamar El-rufai da gwamnnan Katsina suka furta tsayawar takarar Buhari zai amsu a bakin jama’a, amma banda irin gwamnoni na jihar Kogi ko Benue.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel