Bright Chimezi da a ke tuhumar sa tare da Nnamdi kanu, ya roki kotu ta daure Daraktan DSS

Bright Chimezi da a ke tuhumar sa tare da Nnamdi kanu, ya roki kotu ta daure Daraktan DSS

- Tun 14 ga watan Oktoba na 2016 Chimezi ke tsare a hannun Hukumar DSS

- Ya yi wannan roko ne Sakamakon bijirewa umurnin kotu da Daraktan ya yi

- Kotu ta bada umurnin Hukumar ta DSS ta sake Chimezi kuma ta biya sa diyyar naira miliyan 5

Bright Chimezi da a ke tuhumar sa tare da Nnamdi kanu, ya roki kotu ta daure Daraktan Hukumar Tsaro ta Kasa wato DSS, reshen Jihar Akwa Ibom. Ya yi wanna roko ne a kara da ya shigar a wata babbar kotu Uyo, babban birni Jihar Akwa Ibom.

A karar, ya roki a daure Daraktan ne saboda bijire ma umurnin Alkali mai Shari'a Ijeoma Ojukwu da ya yi. Umurnin da Ojukwu ya bayar a ranar 24 ga watan Mayu na 2017 ta ce a saki Chimezi kuma a ba shi diyyar naira miliyan 5.

Bright Chimezi da a ke tuhumar sa tare da Nnamdi kanu, ya roki kotu ta daure Daraktan DSS

Bright Chimezi da a ke tuhumar sa tare da Nnamdi kanu, ya roki kotu ta daure Daraktan DSS

A takardar rokon, Chimezi ya ce jami'an DSS sun kama shi a a gidan sa na Uyo ne a ranar 14 ga watan Oktoba na 2016, amma har ya zuwa yanzun ba'a gudanar da Shari'ar sa ba. Takardar ta kuma nuna yadda ya shigar da kara a babbar kotu na Abuja, na tauye hakkin sa da Hukumar ke yi.

Takardar kuma ta nuna yadda Hukumar DSS ta tabbatar da jawabin sa na kama shi da a ka yi a Uyo, amma Hukumar ta yi jayayyar ba za a gudanar da shari'ar a Abuja ba.

Don haka ne Chimezi ya soke wancan karar na Abuja ya shigar da sabuwa a Uyo. A nan ne Alkali Ojukwu ya bada umurnin sakin sa da biyan sa diyya. Sakamakon kin sakin na sa ne, Chimezi ke rokon a daure Daraktan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel