'Yan Najeriya fiye da 1,000 ke cikin gidan yari a Kasar Thailand

'Yan Najeriya fiye da 1,000 ke cikin gidan yari a Kasar Thailand

- Akwai tarin 'Yan Najeriya da ke kurkuku a can Kasar Thailand

- Jakadan Najeriya a Kasar Alhaji Nuhu Baballiya ya fadi hakan

- Ana kama da dama na 'Yan kasar ne da laifin safarar kwayoyi

Rahoto ya zo mana cewa sama da mutanen Najeriya sama da 1,000 ke garkame a gidajen yari a Kasar Thailand.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Jakadan Najeriya a Kasar Thailand Malam Nuhu Baballiya ya fadi wannan a wani taro da aka gudanar a babban Birnin Tarayya Abuja. Jakadan ya kira 'Yan Najeriya su zama masu halin kwarai a Kasar waje.

KU KARANTA: Wani ya kashe matar sa saboda giyar burkutu

Ko da dai Jakadan bai bayyana laifin da 'Yan kasar su kayi ba amma an saba kama da dama na 'Yan kasar da laifin safarar kwayoyi a Kasar Thailand. Kusan kashi 20% na 'Yan Najeriya da ke kasar su na gidan yari Inji tsohon Jakadan kasar.

Nuhu Bamalli ya bayyana cewa Najeriya na kokarin gyara alakar ta da Kasar Thailand wajen harkar ma'adanai. Najeriya dai tana da albarkatu iri-iri wanda da dama a kan yi fataucin su ne ba bisa ka’ida ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel