Wani mutumi ya bi matar sa har gidan iyayen ta ya kashe ta saboda ta saba masa

Wani mutumi ya bi matar sa har gidan iyayen ta ya kashe ta saboda ta saba masa

- Wani Bawan Allah ya kashe matar sa a cikin Garin Jos

- Yanzu haka dai ana Kotu domin shari'ar da wannan mutumi

- Wannan mutumi ya aikata ta'asar ne a gidan sirikan sa

Hukumar dillacin labarai na kasa NAN ta rahoto cewa an shiga Kotu da wani mutumi saboda ya kashe matar sa da su ke tare da 'ya 'ya 5 tun 2012.

Wannan abu ya faru ne a Garin Langtang da ke Jihar Filaton Najeriya. Wannan mutumi mai shekaru 30 ya aikawa wannan mummunan ta'asa ne a gidan sirikan sa da ke Kauyen Pilgani tun a watan Disamban shekarar bara a kan abin da bai kai ya kawo ba.

KU KARANTA: Wani mutumi ya tsunduma cikin teku a Legas

Ana zargin wannan mutumi ne da aika mai dakin sa har lahira wanda idan aka same sa da rashin gaskiya ana iya aika sa lahirar shi ma. Wannan mutumi dai ya dabawa mai dakin ta sa wuka da gatari ne a jiki kamar yadda ya fadawa 'Yan Sanda da kan sa.

Wannan mutumi ya samu matsala ne da matar ta sa a lokacin saboda ba ta bi umarnin da ya ba ta na hana ta saida giyar burkutu ba a dalilin cewa ya fara lalacewa. Ko da matar ta ki jin na Mijin na ta, sai ya bi har kasuwa inda abin ya kai ga gidan iyayen ta ya kashe ta don haushi!

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel