'Yan Najeriya na kashe kusan Tiriliyan 2.5 a shekara wajen hawa shafin yanar gizo

'Yan Najeriya na kashe kusan Tiriliyan 2.5 a shekara wajen hawa shafin yanar gizo

- Bincike ya nuna cewa ana kashe sama da Tiriliyan 2 a kan salula

- A dai kowane wata akan kashe kusan Naira Biliyan 200 a Najeriya

- Wayar salula na zamani na GSM ta samu karbuwa a fadin Duniya

Kwanaki Jaridar Daily Trust tayi wani bincike game da abin da ake kashewa a Najeriya wajen hawan shafin gizo.

Binciken dai ya nuna cewa a kowane wata ana kashe kusan Naira Biliyan 197 a Kasar nan wajen sayen data wanda ke bada damar a hau shafin yanar gizo a Duniya. Manyan kafofin sadarwar kasar su ne MTN, GLO, Airtel da kuma 9 mobile.

KU KARANTA: Jawabin Shugaba Buhari a wajen taron D-8

Idan dai aka dauki jimillar kudin kusan Tiriliyan 2.5 ake kashewa wajen yakar gizo a kowace shekara. Ana da layukan waya kusan Miliyan 150 a Kasar yayin da ciki dai kasa da Miliyan 100 ke hawa shafin gizo kamar yadda binciken ya nuna.

Idan aka hada da abin da ake kashewa wajen sayen katin waya dabam kuma kudin zai wuce abin da ake tunani. Yanzu haka ma dai karuwa masu amfani da wayar su ke yi a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel