Kotu ta yanke hukuncin bulala 6 kan wani barawon tsani a Abuja

Kotu ta yanke hukuncin bulala 6 kan wani barawon tsani a Abuja

Wata karamar kotu dake unguwar Area 1 a garin Abuja, ta bayar da umarnin tsiyayawa wani Ibrahim Yunusa mai shekaru 28 bulalai har shidda, sakamakon satar tsani da ya yi.

Kotun ta kama Ibrahim da laifin satar ya yin da ya amsa laifin sa kuma ya nemi kotun akan ta yi ma sa rangwami wajen yanken hukunci a kan sa.

Alkalin kotun Alhaji Abubakar Sadiq, ya bayyana cewa barawon ya tsallake hukuncin dauri sakamakon rokon rangwami da ya yi, wanda ya ce ba bu lallai kotu ta sake yi ma sa rangwami idan ya sake gurfana a gaban ta.

Kotu ta yanke hukuncin bulala 6 kan wani barawon tsani a Abuja

Kotu ta yanke hukuncin bulala 6 kan wani barawon tsani a Abuja

Ma'aikaciyar 'yan sanda Misis Florence Avhioboh mai shigar da kara ta bayyanawa kotu cewa, Ibrahim ya aikata wannan laifin ne a ranar 12 ga watan Oktoba da ta gabata, inda wani Jacob Friday mazaunin unguwar Mararaba ta jihar Nasarawa ya shigar da kara a ofishin 'yan sanda na Karmo.

KARANTA KUMA: Ko kusa baka cancanci shugabancin Najeriya ba - Tsohon hadimin Shekarau

NAIJ.com ta ruwaito daga Florence inda ta kara da cewa, an kama Ibrahim da wannan tsani da ya sata a kauyen Dape na garin Abuja, wanda yayin tuntubar sa ya gaza bayar da bayanai kan yadda ya mallaki wannan tsani, ya kuma amsa laifin sa na satar da ya sabawa sashe na 288 na dokar kasa.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel