Kudin Makamai: Bafarawa da dan sa sun gaza samun rabe shari'ar su da ta Dasuki

Kudin Makamai: Bafarawa da dan sa sun gaza samun rabe shari'ar su da ta Dasuki

- Bafarawa da dan sa Sagir sun nemi da rabe shari'ar su da ta Dasuki

- Sun yi korafi kan yadda shari'ar ke fuskantar jinkiri sakamakon rashin bayyanar Dasuki a kotun

- Alkali mai shari'ar ya ki amincewa da rabe shari'ar ta su da ta Dasukin

Wata babbar kotu a Abuja ta ki amincewa rabe shari'ar Sambo Dasuki da shari'ar Attahiru Bafarawa da dan sa Sagir tare da Kamfanin sa a game da maganar wawushe kudin makamai.

A halin yanzun dai Dasuki da Bafarawa tare da dan sa da kamfanin dan na sa da kuma tsohon karamin Ministan kudi wato Bashir Yuguda, su na fuskantar tuhumar laifuka 22 na zamba da almundahanar wawushe kudin talakawa na naira biliyan 19.4.

Kudin Makamai: Bafarawa da dan sa sun gaza samun rabe shari'ar su da ta Dasuki

Kudin Makamai: Bafarawa da dan sa sun gaza samun rabe shari'ar su da ta Dasuki

Bafarawa da Sagir da Yuguda sun yi korafi game da jinkiri da shari'ar ta su take fuskanta sakamakon yawaitan rashin bayyanar Dasuki a wurin shari'ar. Don haka su ka bukaci a rabe shari'ar ta su daga ta shi shari'ar.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa jam'iyyar APC mayar da Tinubu saniyar ware - Doyin Okupe

A nan ne alkali mai shari'ar, Husseini Baba-Yusuf ya ki amincewa kasancewar Dasuki ya bayyana a wurin shari'ar Jiya. Lauya mai shigar da kara ya bukaci a dage shari'ar a inda Alkalin ya dage shari'ar zuwa 6 da 7 ga watan Disamba.

Alkalin ya kuma ce kotun nasa zata yi aiki da duk wani umurni da kotun koli zata bayar a 25 ga watan Janairu na 2018. Sai dai kuma sauraron umurnin ba zai hana cigaba da gudanar da shari'ar ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel