Zambar Naira Biliyan 1.6: Akawun Asusun gwamnatin jihar Kebbi ya yanki tikitin dauri na shekara 70 a gidan kaso

Zambar Naira Biliyan 1.6: Akawun Asusun gwamnatin jihar Kebbi ya yanki tikitin dauri na shekara 70 a gidan kaso

Hukumar EFCC ta taso keyar akawun asusun gwamnatin jihar Kebbi Mohammed Arzika Dakingari, sakamakon kama shi da ta yi dumu-dumu cikin zambar makudan kudin gwamnatin jihar da suka tashi Naira Biliyan 1.6.

Hukumar ta titsiye Dakingari tare da Musa Yusuf wanda shine manajan kamfanin Beal Construction wanda mallakin akawun ne, inda suka yi amfani da wannan kamfani wajen wawushe kudin gwamnatin jihar.

Binciken EFCC da sanadin cibiyar CAC (Corporate Affairs Commision) ya bayyana cewa, Mohammed Bashir Mohammed, Anwal Sadat da kuma Nasir Mohammed duk 'ya'ya ne ga Dakingari, wanda sun kasance daraktoci ne a kamfanin mahaifin na sum sai kuma 'yan uwan sa biyu Abdullahi Mohammed da Habibu Mohammed ragowar masu bayar da umarni a kamfanin.

NAIJ.com ta fahimci cewa, kamfanin ya na amfani da asusun bankuna biyu na Unity da Eco, wanda bincike ya nuna cewa an makire su da Naira Biliyan 1.3 a tsakanin watan Mayu na shekarar 2012 zuwa watan Satumba na shekarar 2013.

Zambar Naira Biliyan 1.6: Akawun Asusun gwamnatin jihar Kebbi ya yanki tikitin dauri na shekara 70 a gidan kaso

Zambar Naira Biliyan 1.6: Akawun Asusun gwamnatin jihar Kebbi ya yanki tikitin dauri na shekara 70 a gidan kaso

Dakingari tare da makarraban sa sun ribaci wasu aikace-aikace na gwamnatin jihar wadanda suka hadar da; ginin makarantar sakandiri ta Mohammed Maira akan kudi naira miliyan 247, aikin ruwa na babban masallacin jihar akan kudi naira miliyan 110 da kuma samar da kayan karatu na makarantun sakandare guda 66 akan kudi naira 987.

KARANTA KUMA: Jawaban shugaba Buhari a taron kungiyar kasashen D-8 na Kasar Turkiyya

Babbar kotun jihar Kebbi ta yankewa manajan kamfanin Musa Yusuf hukunci dauri na watanni shidda a gidan kasa, ta kuma ce Dakingarri ya kama gabansa sakamakon rashin dalilai da suke alakanta shi da aikata laifin.

Hukumar EFCC cikin bin tsarin doka da shari'a, ta ce hakan ba zai yiwu inda ta shigar da korafi a kotun daukaka kara, inda cikin bincike na diddigi ta kama dakin gari da laifuka goma wanda ta yanke ma sa hukuncin daurin shekara bakwai akan kowane laifi da ta kama shi da shi.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel