Abubuwa uku dake birgeni a dandalin Kannywood - Fati SU

Abubuwa uku dake birgeni a dandalin Kannywood - Fati SU

Fitaciyyar ‘yar wasan nan ta Kannywood wacce aka fi sani da suna Fati SU ta bayyana cewaa akwai wasu abubuwa guda uku dake matukar burgeta a dandalinsu na Kannywood.

Ta fayyace wadannan abubuwa ne a lokacin da ta zanta da gidan jaridar Premium Times Hausa.

Fati SU ta yi matukar jinjina wa jaruman kannywood da sauran yan uwanta dake harkar fina-finai a farfajiyar.

Abubuwa uku dake birgeni a dandalin Kannywood - Fati SU
Abubuwa uku dake birgeni a dandalin Kannywood - Fati SU

Ta bayyana abubuwa uku dake burgeta kamar haka:

1. Tallafa wa juna: “Idan har mutun ya kasance a wannan dandali na Kannywood zaka ga ana tallafa wa juna musamman idan mutun ya kasance sabon shiga ne a harkar. Ana amfana da haka mussamman daga gurin wadanda suka kwana biyu a harkar.”

KU KARANTA KUMA: Femi Adesina yace bambancin dake tsakanin Jonathan da Buhari shine yarda

2. Rashin yi wa juna hassada: “Ko da dai kowa da yadda yake duban al’amarin, ni dai a nawa ganin sai dai a sami rashin jituwa amma son juna ya fi yawa a tsakanin mu. Rashin hassada ga juna musamman idan baka jima ba da Fara harkar. Manyanmu zasu yi ta taimaka maka kaima tauraron ka ya shana."

3. Hadin Kai: “Duk inda kaga dan wasa to zaka ga ana tafiya tare ne. Ko da akwai na ciki amma dai ana tare.”

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel