Za a fara tantance tsofin sojoji domin biyansu fansho

Za a fara tantance tsofin sojoji domin biyansu fansho

- 29 ga watan Nuwamba za a fara tantance dukkan tsofin sojoji domin fara biyansu kudadensu na fansho

- Za a gudanar da tantancewar ne domin sanin hakikanin adadin tsofin sojojin da za a biya fanshon

- Tantancewar zata bawa hukuma damar sabunta bayananta tare da kakkabe 'yan fansho na bogi

Hukumar sojin Najeriya tare da hukumar biyan fanshon soji ta bayyana ranar 29 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da zata fara tantance dukkan tsofin sojoji domin fara biyansu kudadensu na fansho.

Za a fara tantance tsofin sojoji domin biyansu fansho

Za a fara tantance tsofin sojoji domin biyansu fansho

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Ikenna Ezendu, ya ce zasu gudanar da tantancewar ne domin sanin hakikanin adadin tsofin sojojin da zasu biya fanshon kuma tantancewar zata dauki kusan sati biyu.

DUBA WANNAN: Cutar tarin kwatai ta yi sanadiyar mutuwar yara 11 a Kano

Ezendu ya kara da cewar tantancewar zata bawa hukuma damar sabunta bayananta tare da kakkabe 'yan fansho na bogi. Hakazalika yayi kira da duk wani dan fansho na bogi da ya nisanta daga zuwa wurin wannan tantancewa domin gujewa gurfanarwa.

A karshe Mista Ezendu ya ce zasu aika da cikakken bayanin yadda tantancewar zata gudana ga hukumar soji domin sanar da wadanda abin ya shafa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel