Yadda wani ɗan sane yayi ma direban ‘A-daidaita-sahu’ sanen waya

Yadda wani ɗan sane yayi ma direban ‘A-daidaita-sahu’ sanen waya

Wata Kotun garin Karmo ta yanke ma wani matashi zaman gidan Yari na tsawon watanni biyar da horo mai tsanani bayan ta tabbatar da laifin satar waya da ake tuhumarsa da shi.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito matashin mai suna Usman Danbaba ya aikata wannan laifi ne a ranar 12 ga watan Oktoba a garin Jabi, inda ya dauke wayar wani direban Keke Napep Ahmed Ali, inda ya kawo kararsa ofishin Yansanda dake Utako, Abuja.

KU KARANTA: Takarar shugaban ƙasa a PDP: Ina Mazan suke – Fayose ga al’ummar Arewa

Bayan ya sace wayar ne sai yayi kokarin dira ya tsere daga Keken kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito, sai dai bayan da yaji matsa a hannun Yansanda, sai ya amsa laifinsa, kuma hakan ya saba ma ma sashi na 28 na kundin aikata laifuka, inji Dansanda mai kara.

Yadda wani ɗan sane yayi ma direban ‘A-daidaita-sahu’ sanen waya

Barawo

Shima a nasa bangaren, wanda ake tuhuma, Usman Danbaba ya amsa laifinsa, kuma ya nemi Kotu tayi masa sassauci.

Bayan sauraron karar, sai Alkalin Kotun, Alhaji Abubakar Sadik ya yanke ma Usman hukuncin zaman gidan yari wata biyar, ko kuma ya baiya taran naira dubu goma, daga karshe kuma ya gargade shi da kada ya sake aikata laifin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel