Takarar shugaban ƙasa a PDP: Ina Mazan suke – Fayose ga al’ummar Arewa

Takarar shugaban ƙasa a PDP: Ina Mazan suke – Fayose ga al’ummar Arewa

- Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose, ya jaddada da takarar sa ta mukamin shugaban kasa

- Fayose ya kalubalanci mutanen Arewa dake jam’iyyar PDP

Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose, wanda tuni ya kaddamar da takarar sa ta neman mukamin shugaban kasa a Najeriya ya kalubalanci mutanen Arewa dake jam’iyyar tasu da su fito a kara idan ba ga tsoro ba.

Wannan kururuwa na gwamna Fayose ya biyo bayan sanarwar da jam’iyyar PDP ta fitar inda tayi watsi da takarar Fayose, domin kuwa ta riga ta mika takarar kujerar shugaban kasa ga yankin Arewa.

KU KARANTA: Mummunan haɗari: Wata babbar Mota ta mitsitstsike wani matuƙin Keke

Jaridar Daily Post ta ruwaito kamar yadda jam’iyyar PDP ta mika takarar shugaban kasa ga Arewa, haka ta mika mukamin kujerar sugaban jam’iyyar ga yankin kudu.

Takarar shugaban ƙasa a PDP: Ina Mazan suke – Fayose ga al’ummar Arewa

Fayose

Sai dai da yake babu wani dan takara daga Arewa daya nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasar, tun bayan da Fayose ya kaddamar da tasa takarar, hakan ne ya bashi daman kalubalantar su.

Majiyar NAIJ.com ta gano wani rubutu da Fayose yayi a shafinsa na Twitter yana cewa “Kamar yadda na nuna muradin takarar shugaban kasa a PDP, ina kalubalantar masu son takarar shugaban kasa da su fito.”

Ko a cikin satukan da suka gabata, sai da shugaban jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi ya jaddada manufar jam’iyyar su ta tsayawa akan dokar rarraba kujerun takara a tsakanin sassan kasar nan.

“Idan kana nukatar tsayawa takarar wata kujera da muka mika tag a yan Arewa, zamu siyar maka da takardar tsayawa takara, don mun sani jama’a da dama sun shirya tsaf don kai mu gaban kotun.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Kalli bidyon kaddamar da takarar Fayose a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel