Ma'aikata na NEMA sun cimma yarjejeniya janye yajin aiki

Ma'aikata na NEMA sun cimma yarjejeniya janye yajin aiki

- Ma'aikatan hukumar NEMA sun cimma yarjejeniyar dakatar da yajin aikin da suka fara a ranar Alhamis

- Ma'aikatan sun shiga yajin ne saboda rashin cika alkawuran inganta bukatunsu

- Mai magana da yawun hukumar ya ce ana sa ran za a sake bude ofisoshin a ranar Juma'a don ci gaba da aiki

Akwai alamu mai karfi cewa ma'aikatan hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), sun cimma yarjejeniyar tare da ministan kwadago, Mista Chris Ngige, bayan shiga wata sabuwar yajin aiki a farkon makon nan.

A ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba ne ma'aikatar hukumar suka fara yajin aiki na kwana uku don nuna rashin jin dadi game da rashin cika alkawari kan inganta bukatunsu bayan wani umarnin da kungiyar ma'aikatan ta bayar a Abuja.

Bayan wannan ci gaba, Dokta Ngige ya kira taron gaggawa tare da ma'aikatan wwwanda baabban darakta Engr. Mustapha Maihaja ya jagoranta da wakilai na kungiyoyin TUC, ASCSN, FCT da kungiyar ma’aikatan tarayyar Najeriya.

Ma'aikata na NEMA sun cimma yarjejeniya janye yajin aiki tare da ministan kwadago

Ofishin hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA

NAIJ.com ta tattara cewa an kammala taron tare da kula yarjejeniyar sulhu wanda bangarorin biyu suka sanya hannu tare da babban sakataren ma'aikatar kwadago a matsayin shaida.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na son kai ga wadanda ba musulmai ba – Matasan CAN sunyi zargi

A cewar kakakin hukumar NEMA, Mista Sani Datti, ana sa ran za a sake bude ofisoshin a ranar Juma'a don ci gaba da aiki, kamar yadda yake cikin sanarwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran

Cacar baki mai zafi ta barke a tsakanin masarautar Saudiyya da kuma jagororin shi'a a Iran
NAIJ.com
Mailfire view pixel