Rikicin Mambilla: An zargin gwamnatin Taraba da wawushe kudin tallafin da Dangote ya bayar

Rikicin Mambilla: An zargin gwamnatin Taraba da wawushe kudin tallafin da Dangote ya bayar

Jama'ar gari da dama dai a jihar Taraba dake a Arewa maso gabashin kasar nan sun yi zargin mahukunta a jihar tasu da wawushe kudaden tallafi da suka kai Naira Miliyan 50 da hamshakin dan kasuwar nan Aliko Dangote ya bayar ga talakawan jihar da rikicin Mambila ya shafa.

To sai dai tuni gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamnan ta Darius Isiyaku sun musanta zargin inda suka bayyana cewa hamshakin dan kasuwar har yanzu bai ba jihar ko sisi ba alkawari kawai yayi.

Rikicin Mambilla: An zargin gwamnatin Taraba da wawushe kudin tallafin da Dangote ya bayar

Rikicin Mambilla: An zargin gwamnatin Taraba da wawushe kudin tallafin da Dangote ya bayar

KU KARANTA: Babban dalilin da ke sa karuwanci na karuwa

NAIJ.com dai ta samu cewa ko a makon jiya sai da wasu shugabanin al’umman yankin Mambillan suka yi korafi na cewa fiye da watanni uku da bada gudummawar, har yanzu su basu ga koda kwandala ba.

Mai karatu dai zai iya tuna kimanin watanni da dama da suka gabata ne dai kazamin rikici ya barke a tsakanin al'ummomin kabilun dake a saman tsaunin Mambilla dake a jihar ta Taraba inda kuma yayi sandiyyar mutumar fulani da ma.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel