Shugabannin jam'iyyar PDP za su gudanar da wani babban taro na musamman 24 ga watan Oktoba

Shugabannin jam'iyyar PDP za su gudanar da wani babban taro na musamman 24 ga watan Oktoba

Shugabannin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya sun tsaida ranar Talata mai zuwa 24 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za su gudanar da muhimmin taron su na kwamitin zartarwar jam'iyyar a babbar hedikwatar su dake a Wadata Plaza babban birnin tarayya Abuja.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu tuni har an sanar da dukkan wadanda abun ya shafa a jam'iyyar game da muhimmin taron da ake sa ran zai tabbatar da babban gangamin jam'iyyar da za'a a watan Disemba 9 ga wata tare kuma da amincewa da bagiren taron.

Shugabannin jam'iyyar PDP za su gudanar da wani babban taro na musamman 24 ga watan Oktoba

Shugabannin jam'iyyar PDP za su gudanar da wani babban taro na musamman 24 ga watan Oktoba

KU KARANTA: Zaben 2019: Hukumr INEC zata dauki ma'aikata miliyan 1

NAIJ.com dai ta samu cewa an fara cece-kuce ne game da wurin da za'a kaddamar da taron ne inda wasu ke so ayi shi a babban birnin tarayya Abuja domin kaucewa shigar shigula da gwamnoni za su iya yi idan har aka kai shi a wata jiha.

Zaben dai na shugabannin jam'iyyar tuni ya dauki zafi inda mutane da dama daga kudancin kasar nan suka nuna sha'awar su ta fitowa musamman ma dai a kujerar shugaban jam'iyyar.

Kadan daga cikin masu takarar shugabancin jam'iyyar dai sun hada da Mr. Jimi Agbaje, Prof. Taoheed Adedoja, Gbenga Daniel, Chief Olabode George, Prof. Tunde Adeniran, Chief Raymond Dokpesi da kuma Prince Uche Secondus.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel