Dalilin da yasa jam'iyyar APC mayar da Tinubu saniyar ware - Doyin Okupe

Dalilin da yasa jam'iyyar APC mayar da Tinubu saniyar ware - Doyin Okupe

- Tsohon hadimin shugaban kasa Goodluck Jonathan, Doyin Okupe yayi zargin cewa jam'iyyar APC bata damawa da Ahmed Bola Tinubu

- Kamar yadda yace Kabilanci ne babban dalilin da yasa jam'iyyar bata dauki Bola Tinubu a bakin komai ba

- Ya bada wasu misalai inda yayi ikirarin cewa Kabilancin ne yasa wasu yan siyasar a baya basu kai labari ba

Hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a fanin kafafen yadda labarai Dr. Doyin Okupe ya bayyana dalilin da yasa jam'iyyar APC ta mayar da Bola Ahmed Tinubu saniyan ware duk da cewa yana daga cikin jiga-jigan da suka kafa jam'iyyar. Hasali ma, ana masa kalon shugaba ne kawai a yankin kudu maso yamma.

Kamar yadda a rubuta a shafinsa na Facebook, yace duk da kasancewar Tinubu musulmi, Jam'iyyar APC bata dauke shi a bakin komai ba, domin nuna wariyar 'Kabilanci' wadda kuma itace matsala mafi girma da ke addabar Najeriya.

Dalilin da yasa jam'iyyar APC mayar da Tinubu saniyar ware - Okupe

Dalilin da yasa jam'iyyar APC mayar da Tinubu saniyar ware - Okupe

Kamar yadda yace "kabilanci yayi wa Najeriya barna fiye da yadda mutane ke tunani. A wasu lokutan mutane suna yin kuskure wajen yiwa kabilanci kallon addini, Kabilanci yafi addini hadasa fitina a Najeriya nesa ba kusa ba.

''MKO Abiola musulmi ne amma da aski yazo gaban goshi, an juya masa baya a matsayinsa na dan jam'iyyar NPN da kuma lokacin da ya zama zababen shugaban kasa karkashin jam'iyyar SDP''

DUBA WANNAN: Jihohin da suke kan gaba wajen yawan bursunoni a Najeriya

Daga karshe Okupe yayi ikirarin cewa babu jam'iyyar adawa a kasan nan yanzu kuma hakan yana daya daga cikin dalilan da yasa Najeriya ta tsinci kanta cikin halin ha'ula'i.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel