Gudun Hijira ba bisa ka'ida ba: Cikin shekara guda 'yan Najeriya sama da mutum 200,000 ne suka tsere, 36,000 sun isa turai ta ruwa

Gudun Hijira ba bisa ka'ida ba: Cikin shekara guda 'yan Najeriya sama da mutum 200,000 ne suka tsere, 36,000 sun isa turai ta ruwa

Dubban Matasa 'yan Najeriya ke tururuwar ficewa zuwa kasashen turai domin neman ingantacciyyar rayuwa duk da hadarin dake cikin hanyoyin irin wannan gudun hijira ba bisa ka'ida ba.

Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar kula da 'yan gudun hijira da kuma 'yan share guri zauna ta bayyana cewar sama da mutum dubu dari 200 'yan Najeriya ne suka tsere zuwa kasashen ketare daban-daban a shekarar 2016. Cikin wannan adadi kimanin mutum dubu 36 sun isa turai ta ruwa.

Kwamishinan hukumar, Sadiya Farouq, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tuntuba a kan gudun hijira da aka gudanar a Legas.

Gudun Hijira ba bisa ka'ida ba: Cikin shekara guda 'yan Najeriya sama da mutum 200,000 ne suka tsere, 36,000 sun isa turai ta ruwa

Gudun Hijira ba bisa ka'ida ba: Cikin shekara guda 'yan Najeriya sama da mutum 200,000 ne suka tsere, 36,000 sun isa turai ta ruwa

A watan Maris na shekarar nan, Najeriya nada sama da mutum miliyan daya da suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira.

DUBA WANNAN: A fito fili a fada: Wata kungiya ta yi kira ga gwamnati da ta baiyana sakamakon binciken kudaden da aka yi wa Babachir

Sadiya ta shaidawa taron cewar hukumar ta na tuntubar kasashen ketare, musamman na turai, domin ganin yadda za a shawo kan matsalar gudun hijira ba bisa ka'ida ba.

Matasa 'yan Najeriya na tururuwar ficewa zuwa kasashen turai domin neman ingantacciyyar rayuwa duk da hadarin dake cikin hanyoyin irin wannan gudun hijira ba bisa ka'ida ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel