Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

- Wata dattijuwa ta fara gani da idanun ta bayan likitocin rundunar sojin Najeriya sun duba ta a jihar Ribas

- Matar mai suna Mrs. Okere ta mika godiyar ta ga Ubangiji kuma ta sanya wa rundunar sojin Najeriya albarka

- Wakilin shugaban hafsoshin sojin Najeriya a jihar, Manjo Janar Rogers Nicholas yace irin wannan aikin taimakon yana daga cikin al'addun rundunar

Wata dattijuwa mai suna Mrs. Margaret Okere ta samu waraka daga makantar da take fama dashi bayan likitocin rundunar sojin Najeriya da ke duba marasa lafiya a Unguwar Umuokwa da ke karamar hukumar Etche sun duba ta.

Hukumar dilancin labaran Najeriya (NAN) ta bada rahoton cewa Rundunar sojin suna gudanar da gangamin karawa al'umma ilimi ne da kuma duba marasa lafiya kyauta wanda ke tatare cikin atisayen da rundunar take gudanarwa a yankin mai taken 'Murmushin Kada 2'.

Uwargida Okere ta shaida wa manema labarai cewa ta dade bata gani da idanun nata amma ta fara gani bayan likitocin sun duba idanun nata, kana suka diga mata magani a idanun bugu da kari su bata tabarau.

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Allah Sarki: Wata dattijuwa ta samu waraka daga makanci sanadiyar aikin agajin lafiya na soji

Uwargida Okere da tace jikanta ne ya kai ta wajen da likitocin suke duba mutane domin ya samu labarin cewa kyauta ne. Ta mika godiyar da ga Ubangiji domin yanzu tana iya gani.

Har ila yau, tayi addu'a da fatan alkhairi ga jami'an rundunar sojin da ke gudanar da atisayen.

DUBA WANNAN: Jihohin da suke kan gaba wajen yawan fursunoni a Najeriya

Bayan Mrs Okere, wasu mutane da yawa sun nuna godiyan su da farin ciki yadda atisayen ya amfane su domin a dalilin hakan sun sami sauki da waraka daga cututuka daban-daban da suke fama dashi.

A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa, Manjo Janar Rogers Nicholas wanda ya wakilci shugaban hafsoshin sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Burai yace dama rundunar ta dade tana yin irin wannan ayyukan taimakawa al'umman domin kara samun fahimta tsakanin soji na al'ummar garin.

Ya kuma yi amfani da wannan damar domin musanta zargin cewa magunguna da suke bayar wa yana da wani nasaba da cutar kyandar biri.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel