APC ta caccaki Goodluck Jonathan kan Buhari

APC ta caccaki Goodluck Jonathan kan Buhari

- Jam'iyyar APC maida martani ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan furucin sa da yayi kan gwamnatin Buhari

- Jonathan yace jam’iyya mai mulki na tafiyar da gwamnatinta akan karya da farfaganda

-/ Kakakin jam'iyyar APC, Bolaji Abdullahi ya caccake sa

Kakakin jam’iyyar APC, Mallam Bolaji Abdullahi ya maida martani ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan furucin sa da yayi na cewa jam’iyya mai mulki na tafiyar da gwamnatinta akan karya da farfaganda.

Jonathan a yayinda ya karbi bakuncin daya daga cikin masu neman kujerar shugabancin jam’iyyar PDP, Farfesa Tunde Adeniran a gidansa dake Abuja, yace lallai jam’iyyar PDP, wacce ta yi shugabanaci daga 1999 zuwa 2015 ta taka rawar gani a kasar amma jam’iyyar APC ta gaza ma kasar da mutanen ta.

Da yake maida martani, Abdullahi wanda yayi aiki a gwamnatin Jonathan yace, “Ina kokwato idan har shugaba Jonathan ne ya furta wadannan kalamai da kayi rahoto saboda zai fallasa kansa ne. Sannan abu na biyu, na san tsohon shugaban kasar da halin sa.

“Kwanan nan na karanta cewa yana ba jam’iyyar sa shawara akan irin shugaban kungiya da sakataren labarai da zata zaba. Zantuka irin wannan shine misali na irin hallayar sa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Lamido yayi ganawar sirri da Abdulsami kan kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa

“Amma idan har da gaske ya furta hakan, zance cikin girmamawa yana bukatar Karin sani akan yadda da kuma dalilin daya sa APC ayi nasara a zaben shugabanci na 2015.

“Idan har za’a ce APC tayi nasarar zabe ta hanyar yaudarar mutane ne yayi sauki da yawa kuma hakan na iya zama cin zarafi ga miliyoyin yan Najeriya da suka zabi APC zuwa mulki,” inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel