2019: Lamido yayi ganawar sirri da Abdulsami kan kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa

2019: Lamido yayi ganawar sirri da Abdulsami kan kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa

- Alhaji Sule Lamido ya gana da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar

- Sunyi ganawar ne a gidan tsohon shugaban kasar dake garin Minna

- Hakan na da alaka da kudirin Lamido na son tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019

A ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya gana da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya).

Ganawar na daga cikin ganawar neman shawarwari tare da tsofaffin shugabannin game da kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a 2019.

2019: Lamido na ganawar sirri da Abdulsami kan kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa

2019: Lamido na ganawar sirri da Abdulsami kan kudirin tsayawa takarar shugabancin kasa

Ganawar wanda aka gudanar a gidan tsohon shugaban kasar dake Hilltop Minna, jihar Niger, anyi shi ne cikin sirri sannan kuma sun shafe tsawon sa’o’I biyu.

KU KARANTA KUMA: Direbobi 1500 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP

Koda dai, Lamido baiyi jawabi ga manema labarai ba bayan ganawar, amma majiyoyi sunce shugabannin biyu sun gana sosai akan kudirin Lamido na tsayawa takarar shugabancin kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel