Jihohin da suke kan gaba wajen yawan bursunoni a Najeriya

Jihohin da suke kan gaba wajen yawan bursunoni a Najeriya

Kamar yadda sakamakon wani bincike da hukumar kididiga na kasa ta fitar, jimlan bursunonin da ke gidajen yari a Najeriya shine 68,686. Alkalluman sun nuna cewa akwai cinkoso sosai wadda hakan ya jawo hankalin shugaba Buhari har ma yayi tsokaci akan lamarin inda yace abin kunya ne ga kasar.

Har ila yau, binciken ya gano yawan bursunonin da ke ko wane jiha a Najeriya har ma da jinsin da sukafi yawa, binciken ya nuna akwai maza guda 67,329 sannan mata guda 1,357, ga dai sakamakon bursunonin da ke wasu daga jihohin Najeriya.

1) Jihar Legas

Jihar Legas wadda gari ne na kasuwanci sosai kuma dauke da dimbin jama'a ita ke kan gaba wajen yawan bursunoni a Najeriya wadda yawansu ya kai 7,396 duk da cewa gidan yarin da ke jihan an gina su domin mutane 3,927.

2) Jihar Ribas

Jihar Ribas ita ke biye wajen yawan bursunonin, yawan al'umman da ke zaman gidan wakafi a jihar Ribas shine 4,424 a maimakon mutane 1,354 da ya kamata gidan yarin a dauka.

Jihohin da suke kan gaba wajen yawan bursunoni a Najeriya

Jihohin da suke kan gaba wajen yawan bursunoni a Najeriya

3) Jihar Kano

Jihar Kano da ake ma kirari da tumbin giwa itama ba'a bar ta baya ba wajen yawan bursunonin, kamar yadda binciken ya nuna akwai bursunoni guda 4,183 a garin Kano a maimakon bursunoni guda 2,116 da ya kamata gidajen yarin jihar su dauka.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda tayi nasarar ceto DPO da akayi garkuwa dashi a Neja

Jihohin da sukafi karancin bursunoni kuma sune Jihohin Bayelsa da Ekiti.

Bayelsa na da bursunoni 444 a maimakon 200, ita kuma jihar Ekiti tana da 585 a maimakon 400 a shekaran bara kamar yadda binciken ya nuna. Wannan alkulluman suna nuni da cewa har ma a jihohin da sukafi karancin bursunonin akwai cinkoso sosai a gidajen yarin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji

Naira ta sha kasa yayin da babban bankin Najeriya ya malalo $288miliyan a kasuwar canji
NAIJ.com
Mailfire view pixel