An kashe mana yara 6 da sace mana shanu sama da 200 a Filato – Miyetti Allah

An kashe mana yara 6 da sace mana shanu sama da 200 a Filato – Miyetti Allah

- Kungiyar Miyetti Allah reshen Jos ta koka akan kisan gilla da aka yiwa mutanen ta

- Kungiyar ta ce anyi awon gaba da shanun su sama da 200

- Yan ta'adda kabilan Irgwe ake zargin su da laifin kisan

Shugaban kungiyar makiyaya na Miyetti Allah MACBAN reshen jihar Filato Nura Abdullahi ya zargi mazauna karamar hukumar Bassa da aikata kisan gilla kan ‘yan uwansu guda shida ranar Lahadi.

Ya fadi fada wa yan jaridar PREMIUM TIMES a hirar da yayi da su ta wayar taraho a ranar Laraba 18 ga watan Oktoba inda ya kara da cewa sun sanar wa gidajen jaridu a jihar kan abubuwan da ke faruwa.

Ya kuma ce sun sanar wa jami’an tsaron (‘yan sanda da sojojin ‘Operation safe heven’) da ke karamar hukumar Bassa kan abin da akayi wa ‘yan uwansu a kauyen.

An kashe mana yara 6 da sace mana shanu sama da 200 a Filato – Miyetti Allah

An kashe mana yara 6 da sace mana shanu sama da 200 a Filato – Miyetti Allah

“‘Yan ta’addan Irigwe ne suka far ma wasu makiyaya shida yayin da suke kiwo, suka kama su suka kashe, daga nan kuma suka gudu da shanun su.

KU KARANTA : Buhari ya nuna damuwar sa akan taimakon da yan kungiyar Boko Haram suke samu daga kungiyar yan ta’adar ISIS

"A takaice dai iyalen wadannan makiyaya 6 da aka kashe sun yi hasaran dabobi 232.”

Bayan haka shugaban kungiyar matasan Irigwe dake karamar hukumar Bassa Sunday Abdu ya mai da wa MIYETTI in da ya ce ”Na yi bakin ciki matuka yadda Nura abokina ya zargi mutane na da aikata wannan kisa ga ‘yan uwwan su.”

”Babu kiyyaya Tsakani na da Nura amma ina so duniya ta sani cewa Fulani da muka basu wuri suka zauna tare da mu a kwanakin baya sune a yau suke kashe mu tun a cikin watan da ya gabata batare da wani dalilai ba.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel