Adu’a kadai ba zai kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya ba – Raveren Martins Adewale

Adu’a kadai ba zai kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya ba – Raveren Martins Adewale

- Rev Martins Adewale ya bayyana hanyoyin kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya

- Adewale ya ce yaki da cin hanci da rashawa ya zama dole akan kowani dan Najeriya

- Cin hanci da rasahwa annoba ce da ta addabi kowa a Najeriya

Shugaban cocin Katolika na jihar Legas, Raveren. Adewale Martins, ya ce adu’a kadai ba zai kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya ba.

Martins ya bayyana haka ne a wata taro da ya halarta mai taken: ‘Hanyoyin magance cin hanci da rashawa a Najeriya.

Adu’a kadai ba zai kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya ba – Raveren Martins Adewale

Adu’a kadai ba zai kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya ba – Raveren Martins Adewale

Adewale yayi kira da yan Najeriya da su cire son zuciya, kabilanci, da nuna bambancin addini wajen yaki da cin hanci da rasahawa, saboda cin hanci da rashawa annoba ce da ta addabi kowa da kowa ne a kasar.

KU KARANTA : APC ta bayyana yadda za ta fidda dan takaran shugaban kasa

Adewale y ace, yaki da cin hanci da rashawa ya zama dole akan kowani dan Najeriya, in da gaske muke muna bukatar cigabar kasar mu.

Raveran Matin Adewale yakara jadada cewa “Kafin mu samu nasara wajen yaki da cin hanci da rasahawa a Najeriya dole sai mun ajiye bambancin addini, kabilanci da son zuciya a gefe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Zaben 2019: Ba za mu ba Atiku tikitin takarar mu ba kai tsaye - Jam'iyyar PDP

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel