Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umarnin kwace wasu kadarorin alfarma 14 mallakar tsohon ministan Abuja Bala Mohammed

Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umarnin kwace wasu kadarorin alfarma 14 mallakar tsohon ministan Abuja Bala Mohammed

A yau laraba wata babbar kotu mai zamanta a Abuja ta yanke hukuncin kwace wasu kadarorin alfarma guda 14 mallakar tsohon ministan Abuja, Bala Mohammed.

Dukkan kadarorin dai na unguwannin kece raini ne a cikin kwaryar Abuja, kuma an gano cewar tsohon ministan da dansa Shamsudden ne keda mallakinsu.

Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umarnin kwace wasu kadarorin alfarma 14 mallakar tsohon ministan Abuja Bala Mohammed

Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umarnin kwace wasu kadarorin alfarma 14 mallakar tsohon ministan Abuja Bala Mohammed

Da yake yanke hukunci, mai shari'a Nnamdi Dimgba, ya bayyana cewar kwace kadarorin na wucin gadi ne tare da umartar hukumar EFCC ta wallafa kwace kadarorin a jaridu ga duk wani mai korafi ko ikirarin cewar kadarorin mallakinsa ne ko dalilin da zai hana gwamnatin Najeriya kwace kadarorin.

DUBA WANNAN: Labari da duminsa: Aminu Atiku Abubakar, da ga tsohon mataimakin Obasanjo, zai kwana kurkuku, bisa wannan zargi, karanta

Lauyan hukumar EFCC, Ben Ikani, ya mika bukatar hukumar ta kwace kadarorin tsohon ministan na wucin gadi kuma kotun ta amince.

Ku biyo Naijcomhausa domin karin bayani a kan wannan rahoto.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel