Buhari ya bayar da umarnin biyan Fansho ga 'yan sanda da suka halarci yakin basasa

Buhari ya bayar da umarnin biyan Fansho ga 'yan sanda da suka halarci yakin basasa

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya bayar da amincewar sa wajen biyan Fansho ga jami'an 'yan sanda wadanda suka marawa 'yan sandan Biyafara baya a lokacin yakin Basasa da ya afku a kasar nan shekaru kusan hamsin da suka gabata.

NAIJ.com ta fahimci cewa wannan jami'an 'yan sandan sun samu afuwar shugaban kasa a shekarar 2000 bayan wannan babban laifi da suka aikata.

A ranar Larabar yau, Cibiyar Fansho ta Pension Transitional Arrangement Directorate, PTAD, ce ta bayar da sanarwar inda kimanin 'yan sanda 162 da suka ajiye aiki tare da masu cin gajiya 57 za su samu alfanun wannan kudaden a karo na farko da gwamnatin za ta fara rabawa a wannan wata na Oktoba.

Buhari ya bayar da umarnin biyan Fansho ga 'yan sanda da suka halarci yakin basasa

Buhari ya bayar da umarnin biyan Fansho ga 'yan sanda da suka halarci yakin basasa

Sanarwar ta zo da sanadin ta kamar haka, "Al'ummar Najeriya za su iya tunawa da yakin Basasa da ya afku a tsakanin watan Yuli na shekarar 1967 da watan Janairu na shekarar 1970, wanda sakamakon wannan ibtila'i ne ya jefa wasu mambobin soji, jami'an 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da suka yaki Najeriya karkashin lemar Biyafara wanda hakan ya sanya aka sallame su daga aiki."

Wannan sallamar jami'an ne ta juye zuwa ajiye aiki wato riyata sakamakon afuwa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi musu a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2000.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya ci gaba da amincewa da inganta zamantakewa ta Neja Delta

Cibiyar Fansho ta PTAD ta tantance wannan jami'ai da suka samu afuwar gwamnati tare da hadin gwiwar hukumar 'yan sanda ta kasa.

A sakamakon adalci irin na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin biyan kudaden fansho a gare su tare da biyan masu cin gajiyar wasu daga cikin su da suka riga mu gidan gaskiya.

Cibiyar ta Fansho za ta fara biyan wannan kudaden ga wadanda suke a mataki na farko a ranar Jumma'a 20 ga watan Oktoba na shekarar 2017 jihar Enugu.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019

Batan-baka-tan-tan: Jam'iyyar PDP ta sarewa Atiku gwuiwa game da batun takarar sa a 2019
NAIJ.com
Mailfire view pixel