Canja fasalin Najeriya: Sarkin Kano da wasu sararkunan gargajiya na son gwamnati ta kafa kotuna karkashin masarautu

Canja fasalin Najeriya: Sarkin Kano da wasu sararkunan gargajiya na son gwamnati ta kafa kotuna karkashin masarautu

Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, da sarkin Onitsa, Mai Martaba Nnaemeka Alfred Achebe sunyi kira ga gwamnati data mayar da kotuna da shari'a karkashin masarautu domin samun saukin tsadar tafiyar da kotunan karkashin gwamnati, suna masu bayyana cewar mayar da kotunan karkashin masauratun zai inganta bangaren shari'a domin babu cin hanci a masarautu.

Sarakunan sun bayyana cewar ya kamata gwamnati ta shigar da masarautu cikin harkokin tafiyar da gwamnati domin bunkasa tattalin arziki.

Canja fasalin Najeriya: Sarkin Kano da wasu sararkunan gargajiya na son gwamnati ta kafa kotuna karkashin masarautu

Canja fasalin Najeriya: Sarkin Kano da wasu sararkunan gargajiya na son gwamnati ta kafa kotuna karkashin masarautu

Sunyi wannan kira ne a wani taro da suka halarta a kan rawar da masu rike da sarautar gargajiya ke takawa wajen warware rigingimu domin habaka tattalin arziki a Legas.

DUBA WANNAN: Magidanci ya dawo gida bayan ya tsere da matarsa ta haifi 'ya'ya uku rigis

Sarkin Kano, wanda ya sami wakilcin Sarkin shanun Kano, Alhaji Shehu Mohammed, ya bayyana cewar ya kamata a bawa masarautu damar taka rawa a duk matakan gwamnati musamman idan aka yi da la'akari da irin rawar da suke takawa a fannin tsaro da tattalin arziki a masarautun su.

Hakazalika Sarkin Onitsa, Mai Martaba Achebe, ya ce masauratun sun taka muhimmiyar rawa wajen hada kan jama'a tare da dinke al'umma wuri guda musamman ta baiwar da suke da ita ta sanin bukatun tare da wayar da kan jama'a.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

Kungiyar ‘yan fensho ta gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar ‘ya’yanta 300

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel