Tsagerun Neja-Delta sun yi gaba da wasu Turawa a Najeriya

Tsagerun Neja-Delta sun yi gaba da wasu Turawa a Najeriya

- An sace wasu Turawa a Yankin Neja-Delta kwanan nan

- Wannan abu ya faru ne a Jihar Delta da ke Kudancin kasar

- Rundunar Sojin Najeriya dai na kokarin yakar tsageru

Kwanan na wasu tsageru a Yankin Neja-Delta su ka sace wasu Turawa 4 daga Kasar Ingila kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar The Cable.

Wannan mummunan abu ya faru ne a Garin Burutu da ke Jihar Delta da kimamin karfe 2 na dare a karshen makon jiya. Daga cikin wadanda aka sace akwai wani David Donovan, Chilley Donovan, da kuma wata Alana da ‘Yar uwar ta Tyan.

KU KARANTA: Mahaifiyar wani babban Malami ta rasu a Najeriya

Turawan sun zo kasar ne domin timakawa Jama’ar Yankin da magunguna kyauta. Jami’an ‘Yan Sanda dai sun ce su na bakin kokarin su na ganin an ceto wadannan Bayin Allah. Jami’an tsaron dai sun ki bayyana halin da Turawan ke ciki.

Kwanaki kun ji cewa Sojojin Najeriya ta zuba Runduna guda a Yankin kudancin Najeriya domin inganta tsaro inda satar jama’a yayi kamari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano

‘Yan fensho sun yi zanga-zangar rashin amincewa da mutuwar mambobin su 300 a Kano
NAIJ.com
Mailfire view pixel